Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kungiyar Taliban Sun Rubuta wa Amurkawa Wasika


Wasu mayakan sa-kai a Afghanistan
Wasu mayakan sa-kai a Afghanistan

Kungiyar mayakan Taliban ta rubuta wata wasika zuwa ga Amurkawa da nufin jan hankulansu kan halin da dakarun Amurka ka iya shiga a Afghanistan.

Kungiyar Taliban a wata budaddiyar wasika da ta rubutawa Amurkawa, ta yi kira akan a hau teburin shawara don kawo karshen yakin da aka dade ana yi a Afghanistan.

Kungiyar ta kuma yi ikrarin cewa hare-hare ta sama da dakarun Amurka ke kai wa ba su sake kwato ko da taki daya daga hannun mayakan sa-kan ba.

A yau Laraba, mai magana da yawun kungiyar Taliban Zabihulla Mujahid, ya rarraba wasikar mai shafi 10.

Wasikar ta yi ikrarin ba da cikakken bayani akan nasarorin da kungiyar ta samu da kuma abin da ta kira gazawar hadakar dakarun da Amurka ke jagoranta, yanzu shekaru 17 kenan.

Wasikar ta ‘yan Taliban na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke kara kaimi wajen kai hare-hare akan mayakan don goyon bayan dakarun Afghanistan ta kasa da ta sama, a karkashin sabuwar dabarar yaki a kasar da shugaba Donald Trump ya fitar da zimmar hakan zai kai ga tilastawa ‘yan Taliban hawa teburin shawara.

A wata ziyara da ya kai a gabashin Afghanistan cikin makon da ya gabata, Janaral John Nicholson, kwamandan dakarun Amurka da na NATO a yakin da ake yi a Afghanistan, ya ce zafafa hare-hare da aka yi yayi tasiri.

Koda yake, wasikar ta ‘yan Taliban ta jefa alamar tambaya akan wadannan bayanan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG