Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasuwa Na Ci Gaba Da Kokawa Kan Ci Gaba Da Rufe Iyakar Najeriya Da Nijar


Rufe Iyakar Najeriya Da Nijar Yana Shafar Tattalin Arzikin Yankunan Kan Iyakar
Rufe Iyakar Najeriya Da Nijar Yana Shafar Tattalin Arzikin Yankunan Kan Iyakar

Ci gaba da rufe iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar sakamakon takunkumin kungiyar ECOWAS na ci gaba da haifar da illa ga tattalin arzikin Najeriya musamman arewa maso yammacin kasar.

Yayin da takunkumin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma ta ECOWAS ta kakabawa Jamhuriyar Nijar ke ci gaba da wanzuwa, gwamnatin Najeriya har yanzu ba ta karba kiraye-kirayen da 'yan kasuwa suka jima suna yi mata ba, na ta duba yiwuwar bude iyakokin ta da Jamhuriyar Nijar, saboda amfanin da ke tattare da hakan wajen kara habaka kasuwanci musamman a arewacin Najeriya.

Har yanzu akwai manyan motoci makare da kaya a wasu iyakokin kasashen biyu, wadanda rufe iyakokin ya rutsa da su.

Rufe Iyakar Najeriya Da Nijar Yana Shafar Tattalin Arzikin Yankunan Kan Iyakar
Rufe Iyakar Najeriya Da Nijar Yana Shafar Tattalin Arzikin Yankunan Kan Iyakar

Iyakar shigowa Najeriya daga Nijar ta Lolo a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya, ta kasance daya daga cikin iyakokin da yanzu haka akwai manyan motoci makare da kaya, wadanda rufe iyakokin ya rutsa da su kuma har yanzu direbobin motocin na nan suna jiran tsammani na lokacin da basu tabbas a kan sa, wato na bude iyakokin.

Umar Yusuf direban terala ne da ya fito daga Nijar, rufe iyakar ya rutsa da shi, a iyakar ta Lolo, kuma har yanzu yana nan kan iyar. Ya ce sun dade suna fama da yunwa da sauro a yayin da suke jiran ytsammanin sake bude kan iyakokin don su sami ketarawa da kayayyakin da suka dauko.

Shima Ali Abuo direba ne da matsalar ta shafa, ya ce nan suke kwana nan suke tashi ga yunwa babu abinci. A kan haka ya roki gwamnatin Najeriya da ta duba yiwuwar bude iyakar su samu su bar wurin.

Masu ruwa da tsaki ga harkar huldayya tsakanin Najeriya da kasashen ketare na ganin ci gaba da rufe iyakokin tamkar ci gaba da gurgunta tattalin arzikin arewacin Najeriya ne, da ma huldayyar mutanen kasashen biyu.

Shugaban kungiyar masu fiton kaya na Arewa maso yammacin Najeriya Aminu Dan Iya, ya jaddada kira ga gwamnatin Najeriya da ta duba halin da jama'a suke ciki a yau, ta bayar da dama ga masu kayan da ke kan iyakokin kasar su biya haraji don kayan su shigo cikin kasa.

Rufe Iyakar Najeriya Da Nijar Yana Shafar Tattalin Arzikin Yankunan Kan Iyakar
Rufe Iyakar Najeriya Da Nijar Yana Shafar Tattalin Arzikin Yankunan Kan Iyakar

Suma masu kasuwanci da ma al'ummomin da ke zaune a kan iyakokin har yanzu basu yi kasa a gwiwa ba na fatar da suke da ita ta ganin an bude iyakokin.

Iyakokin Najeriya a Jamhuriyar Nijar dai a can baya sun kasance wuraren da ake hada-hadar kasuwanci, shigowa da fitar da kaya da samar da ayukan yi ga 'yan kasa, amma tun rufe su lamarin ya sauya kuma ba wanda zai ce ga lokacin da za a bude su.

Saurari sautin rahoton Muhammad Nasir:

Rufe Iyakar Najeriya Da Nijar Yana Shafar Tattalin Arzikin Yankunan Kan Iyakar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG