Masu sauraronmu assalamu alaikum; barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na AmsoshinTambayoyinku.
TAMBAYA 1:
“Salam VOA; mu na son ku kalato mana kadan daga cikin tarihin fusataccen sojan nan na Nijar, wanda ya hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum, wato Abdourahamane Oumar Tchiani.”
MASU TAMBAYA: Sanoussi Madattai Damagaram da Issoufou Makeri Madattai Damagaram.
TAMBAYA 2:
“ Assalamu alaikum. Zuwa ga Filin Amsoshin Takardunku na Sashen Hausa. Don Allah Ku tambayar min masana meye TikTok; kuma ya ake amfani da shi. Da fatan za a taimaka a amsa min wannan tambaya. Na gode .”
MAI TAMBAYA: Daga Ishaq Abdullahi Dan Rimi Bena, a karamar hukumar mulki ta Wasagu-Danko a jihar Kebbi, Najeriya.
AMSA 1:
To bari mu fara da amsar tambaya kan tarihin Shugaban Gwamnatin Mulkin Sojan Nijar, Janar Abdourahamane Oumar Tchiani. Idan masu tambayar, Sanoussi Madattai Damagaram da Issoufou Makeri Madattai Damagaram, na saurare, wakilinmu a Agadez, Hamidan Mahamud, ya hado ma ku amsa.
AMSA 2:
Sai kuma amsar tambaya kan kafar sada zumunta ta Tik Tok. Idan mai tambayar, Ishaq Abdullahi Dan Rimi Bena, da ma sauran masu sha’awar ji, na tare da mu, wakilinmu a shiyyar Adamawa da Taraba, a Najeriya, Muhd Salisu Lado, ya samo maku amsa daga Dr Adamu Babikkwai, malani a kwalejin huras da malamai ta gwamnatin tarayya da ke Yola, Adamawa Najeriya.
Sai mako mai zuwa, idan Allah Ya kaimu.
A yi saurare lafiya:
Dandalin Mu Tattauna