Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasuwa Daga Arewacin Najeriya Na Kokawa Kan Kalubale Da Suke Fuskanta A Kudu


Wata kasuwar kayan gwari a Abuja
Wata kasuwar kayan gwari a Abuja

Yayin da gwamnatin Najeriya ke cewa tana daukar matakai domin bunkasa ayukkan kasuwanci da habaka tattalin arziki, wasu 'yan kasuwa na kokawa akan cewa har yanzu suna fuskantar kalubale da ke yin tarnaki ga kasuwanci da kuma tattalin arzikinsu.

Wannan na zuwa ne lokacin da 'yan Arewacin Najeriya dake kasuwanci a yankin Kudu ke cewa suna fuskantar kalubale nau'o'i daban daban.

Masu kasuwanci a kudancin Najeriya wadanda ke kasuwar Mile 12 inda ake hada-hadar kayan gwari, sun ce akwai kalubale da yawa da suke fuskanta kuma wadanda kan kawo koma-baya ga kasuwancinsu da ma tattalin arzikin Najeriya.

Babban Magatakardan Kasuwar Mile 12, Idris Balarabe, yace daga cikin abubuwan da kan ci musu tuwu a kwarya akwai batun tsadar man fetur wanda da shi manoma ke amfani wajen noma da sufurin kayan su zuwa kurmi.

Bayan wannan matsala, Babban Magatardan kasuwar yace akwai wani ibtila'i da ya fada kasuwar kwananan aka rufe ta, abinda ya ja musu asara babba.

Shugaban kungiyar masu noma da kasuwancin kayan albasa na Najeriya Aliyu Isa Samama na cikin masu kokawa akan matsalolin da suka yi tarnakin ga hada-hadar kayan gwari daga yankin arewa zuwa kudu.

Tun shigowar gwamnati mai ci yanzu a Najeriya, karkashin Shugaba Bola Ahmad Tinubu, ta ke cewa tana fitowa da matakai da shiraruwa na habaka ayukkan kasuwanci da noma da sauran sassa daban daban, sai dai har yanzu a iya cewa 'yan Najeriya ba su soma cin gajiyar wasu shiraruwan ba.

Duba da cewa gwmanatin Najeriya ta kaddamarda wani shiri na dokar ta baci ga noman abinci, wakilin Muryar Amurka, Muhammad Nasir ya tuntubi wasu manoma ko yaya yanayin yake yanzu a wurin su?

Ga karin bayani a rahoton da ya hado.

'Yan Kasuwa Daga Arewacin Najeriya Na Fuskantar Kalubale A Kudu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG