Yau Lahadin nan ne yan kasar Tunisia suke zaben shugaban kasar, kai tsaye tun juyin juya halin da aka yi a kasar a shekara ta dubu biyu da goma sha daya data zama sanadin kadawar guguwar neman canji a kasashen Larabawa da kuma wasu yankunan duniya.
An dade an tsumayen zaben na yau da zai kamalla shirin kafa mulkin democradiya a kasar, bayan da yan kasar suka hadasa zanga zanga a duk fadin yankin ta hanyar hambarar da gwamnatin Zine El Abidine Ben Ali shekaru uku da suka shige.
Daga cikin yan takara fiye da goma sh biyu, Beji Caid Essebsi dan shekara tamanin da bakwai shine kan gaba wajen farin jini. Daga shi kuma sai shugaban kasar Moncef Marzouki.
Idan babu dan takara daya samu yawan kuri'un da ake bukata na lashe zaben, za'a zaben fidda gwani a watan gobe na disamba idan Allah ya kaimu.