WASHINGTON, DC —
Masu jefa kuri'u a kasar Switzerland sunyi fatali da shawarar, da ta tanadi, kai tsaye a iza keyar 'yan kasashen wajen da aka samu sun aikata laifi, komin kankantar laifin.
Jiya Lahadi 'yan kasar suka yi watsi da wannan shawara da kashin kuri'ar 59 daga cikin 100, kamar yadda aka samu bayani ta wani shafin yanar gizo.
Jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta Swiss Peoples ko SVP a takaice, ita ta gabatar da wannan shawara.
shawarar da ta tanadin cewa, a iza keyar duk wani dan kasar waje bayan ya gama wa'adin hukuncin da aka yanke masa.
Shugabannin 'yan kasuwa da masu gwagwarmaya, sunce inda akace any na'am da wannan shiri, to zai keta hakkin jama'a da kuma bata dangantaka tsakanin kasar da babbar abokiyar cinikaryarta wato kungiyar kasashen Turai.