Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Jam'iyyun Adawar Congo Na Neman Bijirewa Zaben Kasar


Shugaban Kasar Congo, Denis Sassou Nguesso
Shugaban Kasar Congo, Denis Sassou Nguesso

Mako mai zuwa 'yan jam'iyyun adawar Congo zasu yi taron tantance ko za su tsaya takara a zaben shugaban kasar da za a yi.

‘Yan jam’iyyun adawar kasar Dimukuradiyyar Congo sun shirya za su hadu makon mai zuwa don yanke shawarar ko za su tsaya zaben shugaban kasar ko a’a, wanda aka shirya yi ranar 20 ga watan Maris mai zuwa.

An dais a zaben ne biyo bayan kwaskwarimar da aka yiwa kundun tsarin mulkin kasar ne da ya cire takaita wa’adin mulki, ya kuma bada damar tsayawa na tsawon lokaci a karagar mulkin.

Wanda hakan ya bawa shugaban kasar damar sake tsayawa takara duk da kasancewarsa dan sama da shekaru 70 da haihuwa. A Oktobar da ya shude ne masu zabe suka zabi cire wa’adin mulki karo biyu da zaban tsawon wa’adin mulki.

To amma ‘yan jam’iyyun adawar kasar sun ce duk da an ce kimanin kaso 92 na masuy zaben raba gardamar sun zabi haka, to zaben ba sa kallonsa a matsayin abinda aka yi bisa doka.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG