Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Mutane a Somaliya


Taswirar Kasar Somalia ta Afirka
Taswirar Kasar Somalia ta Afirka

Akalla mutane 2 sun mutu a Mogadishu babban birnin kasar Somalia, lokacin da wani dan kunar mbakin wake ya tada kansa da bam a wani fitaccen gidan cin abinci mai cike da ‘yan jaridu da jami’an gwamnati.

A yau Asabar wakilin Muryar Amurka ya fadi cewa, abin ya faru ne a gidan abincin da ake kira Village Restaurant da yake kusa da fadar shugaban kasar Somalia. Maharin ya tada kansa da yayi sanadiyyar mutuwarsa da kuma wani mutum daya.

Akalla mutane hudu sun jikkata, yawancin ‘yan jaridar da suka bar gidan cin abincin kafin faruwar lamarin sunce, sun ga lokacin da dan kunar bakin waken ke ta kokarin yadda zai tada bam din.

Shekaru 3 da suka wuce dai an taba kai irin wannan hari a wannan gidan cin abincin har sau biyu, daya a Satumbar shekarar 2012 har mutane 15 suka mutu, dayan kuma a watan Nuwambar shekarar 2012 din, nan ma mutane 4 suka mutu a tagwayen harin ranar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG