Mutanen da suka kai harin wani ganao da ya sha da kyar ya ce mutanen dogaye ne kuma suna cikin fararen kaya kodayake akwai wasu sanye da bakaken kaya.
'Yan bindigar sun yiwa kasuwar kawanya ne domin shiga kasuwar daga duk kofofinta. Da suka shiga kasuwar sai suka jefa wani abu kamar guruneti cikin shagon da ake sayar da tufafin mata wanda nan da nan ya kama wuta kafin su soma harbe-harbe na mai kan uwa da wabi. Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun kashe mutane biyar yayin da suma suka rasa mutane biyar cikin wani musayar wuta da jami'an tsaro.
Maharan sun kwace dukiyoyi daga hannun mutane da karfin bindiga. Alhaji Muhammed Nuru shugaban 'yan canji na kasuwar ya ce kawo yanzu dai an kashe mutane da dama domin sun shigo ne daga kowace kofa. Ya ce bayan sun kone kursiyoyin kasuwar sai suka kama harbi kana su 'yan kasuwan suka kama gudu. Ya ce sun bi 'yan canji da bindiga suna fasa akwatunansu suna kwashe kudi. Wadanda kudinsu na cikin sef sai suka sa masu bindiga a ka dole suka bude barayin suka kwashe kudadensu. Ya ce ta wurin gefensa abun da barayin suka sace ba zai kasa nera miliyan ashirin ba. Yanzu suna zaman dar dar ne domin 'yan kasuwa duk sun rufe shaguna sun koma gidajensu.
Ibrahim Abdulaziz nada karin bayani.