Wasu fusatattun ‘yan daba suka mamaye wani yankin Masallacin Idi a ranar Laraba, lamarin da ya haifar da tashin hankali.
Hakan ya biyo bayan wa’adin sa’o’i 48 da gwamnatin jihar Kano ta baiwa ‘yan kasuwar su tashi.
Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano (KNUPDA) ce ta bayar da umarnin dake gargadin cewa an tanadi mumunan mataki ga wadanda suka bijirewa umarnin.
Duk da cewa wa’adin da aka baiwa 'yan kasuwar su tashi ya cika, ‘yan kasuwar sama da budu 5 a kewayen masallacin Idi, sun ci gaba da gudanar da harkokinsu.
Tuni aka tura jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya da na hukumar kula da zirga-zirgar ababan hawa ta Kano KAROTA, zuwa wurin har ma zaman lafiya da kwanciyar hankali sun dawo a yankin na masallacin Idin.
Dalilin da su ka bayar na tashin 'yan kasuwar shine cewar suna zaune a wurin ne ba bisa ka'ida ba.
Dandalin Mu Tattauna