Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kubutar Da Mata ‘Yan kasuwa Da Aka Sace A Kwara


Nigeria Police Force Logo
Nigeria Police Force Logo

Wani yaro mai shekara biyu na daga cikin mutane 12 da rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro a Najeriya ta ceto daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar Kwara a ranar Litinin.

WASHINGTON, D. C. - Wasu masu garkuwa da mutane ne suka yi awon gaba da wasu mata ‘yan kasuwa 11 da suka je kasuwar Oke-Ode da ke karamar hukumar Ifelodun a jihar Kwara a ranar Larabar da ta gabata, tare da yin garkuwa da su a kusa da gadar Oyi da ke kauyen Yaaru-Olayinka.

‘Yan kasuwan dai a cewar majiyoyin sun fito ne daga Offa da Yaaru a jihar Kwara da kuma Ikirun a jihar Osun.

Kakakin Rundunar ’yan sandan jihar Kwara, Ejire-Adeyemi Toun, a ranar Talata, ya ce jami’an tsaro sun ceto mutane 12 ciki har da wani yaro ‘dan shekara biyu.

“Wasu daga cikin wadanda suka samu raunuka yayin aikin ceto an kai su babban asibitin da ke Share, na karamar hukumar Ifelodun kuma an sallame su bayan an yi musu magani.”

Ejire-Adeyemi ya ce, “an kubutar da dukkan wadanda abin ya shafa kuma an mika su ga iyalansu kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Har ila yau, Kodinetan kungiyar tsaro ta hadin gwiwa ta yankin Kwara ta Kudu, Olaitan Oyin-Zubair ya yabawa rundunar hadin guiwar da suka yi aiki wajen kubutar da dukkan mutanen da aka sace.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG