Wakilin mu na jihar Borno Haruna Dauda Biu wanda ya fita titin tsakiyar birnin Maidugurin domin ganewa idanun sa abiinda ke faruwa kuma ya ruwaito cewa yaga mutane da yawa daga inda ake jin wannan karar bindigar na kwararowa cikin gari, wasu ma da kafa suke takowa
Kamar yadda wakilin namu yace wata majiya kwakkwara ta shaida masa cewa anyi barin wuta tsakanin yan kungiyar sa kai da ake kira Civilian JTF da sojojin Najeriya a waje guda suka fatattaki yan kungiyar ta boko haram
Harunan ya kira wasu dake bakin dagan kuma yace yaji ana barin wuta a lokacin da yake Magana da daya daga cikin yan kungiyar Civilian JTF, kuma anyi nasara kan yan kungiyar ta boko haram domin basu samu damar shigowa cikin garin na Maidugiri ba
Wadannan ya boko haram sun kawo wannan harin jim kadan da wucewar shugaba Goodluck Jonathan ya kammala ziyarar sa na kanfe da yazo Maiduguri na neman a sake zabar a a zaben da za ayi watan gobe.
A lokacin wannan kanfe ne ma shughaban yayi alkawarin ganin an kawo karshen kungiyar ta Boko Haram kuma yace insha ALLAHU za’a kwato yan matan Chibok.
A can karamar hukumar Munguno Haruna Dauda yace anyi ta barin wuta tsakanin yan boko haram da sojojin Najeriya da hadin gwiwar civilan JTF suka hana su shigowa garin na Munguno sai Harunan yace ba wata sanarwa daga jamiaan sojojin.