Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mutane 12 Da Suka Hada Da Mata Da Yara A Jihar Neja


Wasu yan bindiga
Wasu yan bindiga

Yan fashin daji na cigaba da aukawa jama'a tare da yin garkuwa dasu domin neman kudin fansa a sassa daban daban na Arewacin Nigeria.

Ko a cikin daren litinin din wayewar garin ranar talata, yan fashin dajin sun auka garin Shadadi ta yankin karamar hukumar Mariga a jihar Neja inda su ka yi awon gaba da mutane goma sha biyu akasarinsu mata da kananan yara.

Al’amarin da ya yi matukar tayar da hankalin mazaunan yankin kamar yadda daya daga cikinsu Alh. Danlami Shadadi ya bayyana. Ya ce, sun kai harin ne da misali karfe daya na rana inda suka yi awon gaba da mata, cikin su harda matan aure da kuma yara.


Rundunar 'yansanda ta jihar Neja dai tace tana bincike akan wannan sabon hari, domin kwamishinan 'yansanda na jihar, Monday Bala Kuryas yace basu gama tantance lamarin ba.

Rundunar 'yan sandan tace ta samu nasarar kama wani mai suna Alh. Bashir Abdullahi da ya kware wajen yin garkuwa da mutane.

A halinda ake ciki gamayyar jami’an tsaron sun samu nasarar kubutar da wasu mutane 22 daga hannun masu garkuwar a kauyen Kuci ta yankin karamar hukumar Muya, kamar yadda wata sanarwa daga ma’aikatar tsaron cikin gida ta jihar Nejan dauke da sanya hannun kwamishinan ma’aikatar, Mr. Emmanuel Umar ta tabbatar.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG