Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari Gidan Gwamnan Jihar Imo


Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma, zagaye da jami'an tsaronsa.
Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma, zagaye da jami'an tsaronsa.

Rahotanni na nuni da cewa wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai hari gidan gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, tare a cinnawa gidan wuta.

A wani rahoto da gidan jaridar Vanguard ya rawaito, na cewa maharan sun yi amfani da makamashin Man Fetur a cikin gidan wanda ya haifar da tashin gobara wadda ta kai ga lalata motoci a cikin harabar.

Wannan hari dai ya faru ne a karamar hukumar Oru East dake jihar Imo, wanda nan ne asalin mahaifar gwamnan, kuma ana zargin jami’in tsaro ya rasa ransa sanadiyyar harin.

Karin bayani akan: jihar Imo, Nigeria, da Najeriya.

Ya zuwa yanzu dai babu wasu ko wata kungiya da ta fito a dauki alhakin harin.

Sashen Hausa na Muryar Amurka ya tuntubi kakakin ‘yan sanda wanda ya ce bada jimawa ba zasu fitar da sanarwa kan harin.

Domin karin bayani saurari hirar Ibrahim Ka’almasi da wakilin sashen Hausa Alphonsus Okoroigwe.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG