Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zamfara: Ma’aikatan Lafiya Sun Yi Barazanar Rufe Asibitin Kwararru Kan Matsalolin Albashi


Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal

Sai dai sun yabawa gwamna Dauda Lawal saboda sabunta gine-gine da kayan aiki a asibitin kwararru na jihar a shirye-shiryen daga likkafarsa zuwa asibitin koyarwa.

Hadaddiyar kungiyar ma’aikatan kiwon lafiya da gamayyar kwararrun ma’aikatan jinya, a asibitin kwararru na Yariman Bakura, dake Birnin Gusau, sun bukaci gwamnatin jihar Zamfara, ta gaggauta fara biyan bashin albashin watanni 6 da suke bi a kan tsarin albashin ma’aikatan jinya (CONHESS) da aka yiwa kwaskwarima ko kuma su tsunduma yajin aiki.

Sun yi wannan kira ne yayin ganawarsu da manema labarai game da bashin da suke bi tun daga watan Yuni zuwa Nuwamban da ya gabata da kuma batun ciyar da ma’aikata gaba da har yanzu gwamnatin jihar bata aiwatar ba.

Shugaban gamayyar kungiyoyin ma’aikatan jiya na shiyar, Kwamred Sani Rabiu, yace kungiyar na kuma bukatar a aiwatar da tsarin biyan kudaden alawus-alawus yadda ya dace kama daga na matsayi dana sadaukarwa da kuma na shiga hatsari dake mafi karancin ke farawa na naira dubu 30.

Gamayyar kungiyoyin ma’aikatan jinyar tace ta lura da wasu kura-kurai wajen biyan albashin watanni Oktoba da Nuwamban da suka gabata wadanda suka kunshi rage matsayi da matakin albashi da kuma dora ma’aikata kan matakin da ba nasu ba.

Sai dai sun yabawa gwamna Dauda Lawal saboda sabunta gine-gine da kayan aiki a asibitin kwararru na jihar a shirye-shiryen daga likkafarsa zuwa asibitin koyarwa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG