Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Ruwan Najeriya Sun Kubutar Da Jirgin Denmark Da 'Yan Fashin Teku Suka Sace A Yankin Ruwan Guinea


Jirgin ruwan sojojin Najeriya
Jirgin ruwan sojojin Najeriya

Jirgin ruwan na kasar Denmark da ya iso gabar tekun Guinea daga birnin Amsterdam, ya ratsa kasashen Ghana, Togo, Najeriya, Kamaru da Congo, kafin ‘yan ta’addan su yi awon gaba da shi.

Hedkwatar rundunar sojin ruwan Najeriya, ta ce dakarunta sun kubutar da wani jirgin katafaren jirgin ruwa da ‘yan fashin teku suka sace a gabar tekun Guinea.

Kakakin mayakan ruwan sojojin na Najeriya Navy Commodore Ayo Olukayode Voughan, ya shaidawa Sashen Hausa na Murya Amurka cewa, ‘yan fashin teku sun afkawa jirgin dauke da manyan makamai a ruwan kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Jirgin ruwan mai suna Monjasha Reformer, bayan da ‘yan fashin tekun suka mai dirar Mikiya sun kuma yi garkuwa da ma’aikatansa su 16.

Jirgin ruwan na kasar Denmark da ya iso gabar tekun Guinea daga birnin Amsterdam, ya ratsa kasashen Ghana, Togo, Najeriya, Kamaru da Congo, kafin ‘yan ta’addan su yi awon gaba da shi.

Daga bisani jirgin yakin sojojin Najeriya mai suna NNS Gongola tare da tallafin jirgin ruwan mayakan Faransa da ke wani aikin hadin gwiwa a yankin, ya sami nasarar kubutar da jirgin da Monjasha.

Ko da yake, ‘yan fashin tekun sun yi awon gaba da ma’aikatan jirgin ruwan guda shida

A halin yanzu, sojojin ruwan na Najeriya sun bazama neman mutane shida da ake garkuwa da su.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina:

Dakarun Ruwan Najeriya Sun Kubutar Da Jirgin Denmark Da 'Yan Fashin Teku Suka Sace A Yankin Ruwan Guinea - 2'43"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00


XS
SM
MD
LG