Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutuwar Wani Soja Ta Haifar Da Cece Kuce Yayinda Rahotanni Ke Cewa Hukumomin Nijer Sun Kama Wasu Sojoji


A jamhuriyar Nijer mutuwar wani soja cikin yanayin hazo a hannun wasu wadanda ba a san ko su waye ba ta haddasa cece kuce a tsakanin jama’a la wani lokacin da wasu rahotanni ke cewa hukumomi sun kadammar da kame kamen jami’an tsaro da farar hula.

Don haka ne jami’an kare hakkin dan Adam suka bukaci mahukunta su fito su yi bayani don kawo karshen rudamin da ake yadawa a kafafen sada zumunta.

Goggon marigayi Mamman Mansour Adamou ta yi wa manema labarai karin bayani dangane da rasuwar jami’in sojan, wanda ake hasashen ya mutu a hannun wasu wadanda suka yi awon gaba da shi a ranar talata 1 ga wata Maris din da muke ciki a nan Yamai. Ta ce bayan da danta ya fita waje, sai ya tarar da sojoji inda suka fara bugunsa duk da yana tambayarsu laifin me ya yi. Dattijiyar ta kara da cewa sa’o'i kadan bayan haka an tarar da gawarsa a mutuware.

Yau kusan mako 1 bayan faruwar wannan al’amari har yanzu ba wani bayani a hukunce. Dalilin da ya sa kenan jami’an kare hakkin dan adam ke jan hankulan gwamnatin Nijer a game da mahimmancin yin bayani akan lokaci.

Malan Sirajo Issa shi ne Jakadan kungiyar kare hakin dan Adam ta IHCR a Nijer. Ya ce abu ne do suke bi sawu da kafa akansa. An bayyana shaidar takardar mutuwarsa, takardar aikinsa da hotonsa da na iyalensa a yanar gizo don bin didigin lamarin.

Wannan na faruwa ne a wani lokacin da masu amfani da kafafen sada zumunta ke yada jita jitar, kama daga sojoji da farar hula da dama wanda kuma har I zuwa wannan lokaci hukumomi ba su yi wa ‘yan kasa bayani akansa ba.

Mun nemi jin ta bakin kakakin gwamnatin Nijer Tidjani Abdoulkadri akan wadannan batutuwa, wayarsa na kadawa amma bai amsa kiran ba kuma har izuwa lokacin aiko da wannan rahoto bai maido kira ba.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:40 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG