Shugabannin kasashen Afrika ta Yamma sun taro ta hoton bidiyo a jiya Litinin domin shawon kan rikicin siyasa a kasar Mali, amma ‘yan adawa sun yi fatali da taron.
Shugabannin adawar kasar sun gaggautar shure wannan yunkuri da shugabannin na Afrika ta Yamma ke yi na tabbatar da shawarwari wanda tuni masu zanga zanga a kasar suka ce ba zasu amince dasu ba.
Shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin Afrika ta Yamma ta ECOWAS, sun yi kira ga shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita, da ya kafa gwamnatin Hadaka kana ya raba madafun ikon kasar. Sai dai abokan adawar sa sun ce ba zasu yarda da duk wani tayi ba, in baicin ya sauka daga karagar mulki, abin da shugabannin Afrika ta Yamma suka ce ba zasu lamunta da hakan ba.
An zabi shugaba Keita ne a zaben shekarar 2013 kana aka sake zaban sa bayan shekaru biyar. Tun daga nan ne kuma farin jinin sa ke kara yin kasa, lamarin da ya kai ga zargin sa da cin hanci da rashawa da kuma gazawa wurin yaki da ayyukan kungiyoyin ta’addan masu tsaurin ra’ayin Islama dake haifar da rashin zaman lafiya a kasar.
Masu sharhi a kan harkokin kasashen Afrika ta Yamma kamar su Farfesa Bube Namaiwa na jami’ar Diof dake Dakar, sun ce hanyar da shugabannin kasa ECOWAS ke bi wurin warware rikicin siyasar Mali ba mai bulla bace dan haka akwai bukatar su sake nazari a kan matakan da suke dauka.
Farfesa Na Mewa, ya ce kudurorin da shugabannin ECOWAS ke dauka a kan wannan batu zai iya kara dagula al’amura, saboda su ‘yan kasar sun ce su ke cikin kasar kuma su suka san matsalar dake addabar kasar.
Ga dai tattaunawar Alheri Grace Abdu da Farfesa Bube Namaiwa a kan rikicin Mali:
Facebook Forum