Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki Da Miyagun Kwayoyi Ba Aikin Mahukunta Bane Kadai


Maryam Ciskuda
Maryam Ciskuda

A shirin mu na siyasa da matasa, yau DandalinVOA ya tattauna ne da matashiya, mai rajin dakile shan miyagun kwayoyi da taimakawa matasa masu tasowa, kauracewa dabi’ar shaye-shayen kwayoyi da bangar siyasa.

Maryam Ciskuda, shugabar kungiyar PG105 da ke yakin wayar da kan matasa masu tasowa, dangane da illar shan miyagun kwayoyi, ta shirya taron karawa juna sani a makarantar Air Force Comprehensive School da ke Kwa a jihar Kano.

Maryam Ciskuda ta ce a kungiyar PG105 suna ba da shawarwari ga matasa wato Parental Guidance, akan illan shan miyagun kwayoyi da wasu dabi’un da matasan su kan tsinci kansu, mussaman a lokacin da suke balaga.

Ta ce a halin da ake ciki yanzu shan miyagun kwayoyin na farawa ne tun daga matakin makarantun sakandire har zuwa girma, har ta kai su ga tsintar kansu a matakin bangar siyasa da makamantan su.

Malama Maryam ta ce wannan ba shi ne taron su na farko ba, shine na uku. Kuma wannan al’ammari na faruwa ne da taimakon abokan arzuki, don babu wata kafa ko kungiya da ke basu tallafi.

Kuma ta ce koda yake a yanzu babu wani asusu ko wata kungiya ta kasar waje da ta ke taimaka musu da kudi ko wasu kaya wajen gani bukatar ta biya, amma bata fitar da ran neman taimako ba a gaba.

A hirar su da wakiliyar DandalinVOA, wata jami’a a hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi Hajiya Aisha Hamidu, ta ce yanzu shan miyagun kwayoyin da ake sha ya ragu, maimakon hakan yan kwaya sun fito da wasu sabbin kwayoyi inda suke hada ababan sha da alewa ko makamanta, domin a bugar da su.

Ta ce kididdigan masu shan kwayoyi akalla ya ragu da kaso 60 cikin dari, sannan hukumomin yaki da shan miyagun kwayoyi, sun fitar da dokokin da idan za’a dauki mutum a aikin gwamnati a jihar Kano, sai an gwada jini shi ko ita domin tabbatar da babu illar miyagun kwayoyi.

Ta kara da cewa haka ofisoshin gwamnati, mukaman gargajiya har ma da 'yan siyasa, duk a jihar Kano ana gwada jinin su kafin a basu ragamar mulkin al’ummarsu.

A saurari cikakken rahoton wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:10:25 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG