Wata matashiya mai sana’ar yin maganin kashe kwayoyin cuta da sabulun wanke mota, Shafa’atu Muhammad, tace idan makarantu da asibitoci da ma’akatun gwamnati suna sayen kayayyakin masu kananan sanao’i, tabbas zai taimaka wajan habakar arzikin al’uma.
Ta bayyana haka ne a yayin da take zantawa da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir, a karamar hukumar Ungogo dake Kanon Dabo a Najeriya.
Ta ce rashin sayan kayyakin da mata a gidaje ke yi domin zama masu dogaro da kai inji matashiya yana kawo wa mata cikas wajan kokarinsu na masu rabuwa da zaman kashe wando.
Malama Shafa’atu Muhammad, mai sana’ar yin maganin kashe kwayoyin cuta da sabulun wanke mota wato'Car wash' ta shafe shekaru fiye da uku tana wannan sana’ar.
Ta kara da cewa sana’ar dogaro da kai na taimaka mata ainun wajan kashe kananan bukatunta na yau da kullum , kuma hakan na rage cece kuce tsakanin maigida da uwargidansa
Ta kuma bukaci gwamnati da ta taimakawa mussamam mata masu kananan sana’oi domin dogaro da kai tare da ingantan tattalin arzikinsu.
Facebook Forum