Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taimakawa Masu Kananan Sana'oi Zai Taba Rayuwar Al'umomi Da Dama


Rakiya Muhammad
Rakiya Muhammad

Wata mai karamar sana’ar dogaro da kai Rakiya Muhammad, ta yi kira ga gwamnati da ta taimakawa masu kananan sana’oi, da kudaden domin su bunkasa harkokin kasuwancin su abinda zai taimaka wajan habakar tattalin arzikin yankunansu.

Ta ce ta shafe shekaru fiye da shida tana yin aikin abinci a karkashin wasu, kafin daga bisani ta bude nata da kudaden albashinta da take tattali .

Tana mai cewa inda gwamnati ta taimakawa masu kananan sana’oi, to tabbaci hakika zai taba rauyuwar al’umomi da dama kuma zai rage zaman kashe wando.

Rakiya ta ce sana'ar hannu wata hanya ce da mace ke tallafawa kanta ba tare da ta dogara a kan mijinta ba, ku kuma ‘yan uwa ba.

Ta kara da cewa a yanzu da ta bude sana'arta na kanta suna kula da sana'ar ne tare da 'yayanta, bayan da ta tara 'yan kudadenta ta hanyar yin adashi domin tara jarinta.

Rakiya ta kara da cewa , bata bada bashi a sana'ar ta domin sana'ar bata yi kwari ba kuma tana jadadda masu saye babu bashi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG