Rahotanni daga Najeriya na cewa gwamnatin tarayya tana wata ganawa cikin sirri da wakilan kungiyoyin kwadago, a wani yunkuri na kaucewa shiga yajin aiki a gobe Talata.
Kungiyoyin na kwadago sun sha alwashin shiga yajin aikin idan har ba a fara biyan ma’aikata N30, 000.00 a matsayin albashi mafi karanci.
A baya, wakilan hadakar kungiyoyin kwadago da na ‘yan kasuwa a Najeriya sun kauracewa wani taro da gwamnatin tarayya ta kira domin kaucewa yajin aikin da kungiyoyin ke shirin yi, kamar yadda jaridun kasar suka ruwaito.
A farkon makon da ya gabata, kungiyar Gwamnoni ta yi tayin biyan N24,500.00 amma kungiyoyin na kwadago suka ki amincewa.
Masu lura da al’amura da fashin baki a fannin tattalin arziki, sun nuna fargabar cewa yajin aikin zai iya yin mummunan tasiri akan tattalin arzikin kasar.
Ma’aikata a Najeriya na karbar N18,000.00 a matsayin albashi mafi karanci, albashin da rahotanni ke cewa wasu jihohin ma ba sa iya biya.
Facebook Forum