Gwamnan jihar Neja kuma shugaban gwamnonin arewa yayi jawabi a taron farfado da tattalin arzikin arewa. A cikin jawabinsa yace tattalin arzikin yankin arewa ba zai farfado ba sai an murkushe ta'adanci da yanzu ya addabi yankin. Gwamnan yace suna fata suna kuma rokon gwamnatin tarayya ta tabbatar nan da wata uku ta kawo karshen ta'adanci a kasar.
Amma dan majalisar wakilai daga jihar Katsina Ahemed Babba Kaita ya nuna tantama akan batun. Yace tattalin arziki na habaka ne akan abun da kasa ta shimfida. Yayi misali da kasar Malyasia inda al'ummar kasar suka fara gyara halayensu da yadda suke gudanar da abubuwa kafin su kama hanyar cigaba. Yace sabo da haka cewa ofishin jakadancin Amurka da 'yan kasuwa da gwamnonin arewa suna taron farfado da tattalin arziki shi bai daukeshi wani abu ba. Yace taron bai wuce na shan shayi ba. Yace abu na daya gwamnoni sun kusa kare wa'adin mulki da suke yi yanzu. Abu na biyu kuma ina makudan kudaden da ake baiwa gwamnonin wadanda biliyoyin nerori ne. A arewa gwamnoni kadan ne suka taka rawar a zo a gani. Yace duk taron yaudara ne. Sai dai a yi fatan Allah ya sa wadanda zasu biyo bayansu zasu yi adalci.
Ga rahoton Medina Dauda.