Sakamakon yadda matsalar tsaron ke neman zama ruwan dare a iyakokin kasashen ya sa hukumomi a Nijar kiran taron na zaman lafiya, domin tunkarar wannan matsalar ta yadda zasu samu fahimtar juna a tsakanin kasashen Nijar da Chadi da kuma Libiya.
Taron dai ya hada dukkan masu ruwa da tsaki da jami'an tsaro da kuma wakilan al'umma da kuma kabilun da ke rayuwa a iyakokin kasashen.
A wani mataki na neman zaman lafiya a arewacin Nijar da ke iyaka da kasashen Libiya da Chadi, hukumomin mulkin soja a Agadas sun gudanar da wani taron zaman lafiya, inda suka tattauna da shugabannin al’ummomi na yankin a fannoni da dama, musanman irin gudunmawar da zasu bayar wajen shawo kan matsalar tsaro da ake fuskanta a cikin yankuna da dama na kasar Nijar.
Abubakar Jerome, magajin garin yankin Dirkou mai iyaka da kasar Libiya, ya bayyana fatan ganin sun yi aiki tare da kasashen Libiya da Chadi wajen magance matsalar tsaro a tsakanin su.
Jagororin al’umma da kungiyoyin fararan hula sun dauki alkawura na kawo nasu taimako a shawo kan matsalar tsaro.
Kwamitin zaman lafiya na yankin Tchiro da ke cikin jihar Agadas na ganin akwai bukatar a samar da wani tsari na fahimtar juna tsakanin al’umma, wanda hakan zai sa ayi watsi da tsauraran akidu da kuma neman taimakon kowa wajen magance matsalar tsaron.
Mahalarta taron sun bukaci ga jagororin mulkin sojan kasar Nijar da su kara azama wurin ganin gwamnati ta dakile sabuwar matsalar tsaron dake fuskantar yankin.
Saurari cikakken rahoton Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna