Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma’aikata Miliyan 255 Ne Suka Rasa Ayyukansu A 2020 – MDD


Kasuwar unguwar Oyingbo a jihar Legas (Reuters)
Kasuwar unguwar Oyingbo a jihar Legas (Reuters)

A cewar babban sakataren majalisar, hakan daidai yake da tafka asarar dalar Amurka tiriliyan 3.3.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla ma’aikata na dindindin miliyan 255 suka rasa ayyukansu a bara sanadiyyar annobar coronavirus.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Babban Sakataren Majalisar Antonio Guterres ya yi kira ga kasashen duniya da su kara kaimi wajen samar da ayyukan yi ga jama’arsu.

Hakan a cewar Guterres, zai taimaka wajen farfadowar kasashen duniya a tare ba tare da an bar wata kasa a baya ba.

“Kiyasi ya nuna cewa ya nuna cewa an rasa sa’a kashi 8.8 na yin aiki, wanda ya daidai da sa’o’i da aka rasa a shekara guda na ayyuka miliyan 255 a 2020.” Guterres ya ce.

“Sanadiyyar wannan annoba, an kiyasin akwai karancin ayyukamiliyan 75 a 2021 sama da abin da aka yi kiyasin gabanin annobar – sannan an ga raguwar ayyuka miliyan 23 da aka yi kiyasin za a iya gani a 2022 gabanin barkewar annobar.”

A cewar babban sakataren, hakan daidai yake da tafka asarar dalar Amurka tiriliyan 3.3 ta hanyar samar da ayyukan yi baya ga tallafin gwamnati.

Guterres y ace wata hanya da za a iya magance wannan matsala ita ce, kasashen su kara mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi akalla miliyan 400 tare da samar da hanyoyi kare su sannan an samar da cikakkiyar kariya ga mata, maza, yara biliyan hudu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG