Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Katsewar Intanet Ta Shafi Sassan Duniya


Yadda fasinja suka yi carko-carko a filin tashin jirage a kudancin London London, Yuly 19, 2024.
Yadda fasinja suka yi carko-carko a filin tashin jirage a kudancin London London, Yuly 19, 2024.

Kazalika matsalar ta shafa har da wasu kafafen yada labarai wadanda suka kasa watsa shirye-shiryensu.

Katsewar intanet a sassan duniya ta haifar da tarnaki inda aka dakatar da tashin jirage, ayyukan bankuna suka tsaya yayin da wasu aikace-aikacen asibitoci ma suka tsaya cik.

Kamfanin CrowdStrike mai tsaron yanar gizo a ranar Juma’a ya ce ba batu ne na tsaro da ya shafi kutse ba.

Kazalika matsalar ta shafa har da wasu kafafen yada labarai wadanda suka kasa watsa shirye-shiryensu.

A cewar AP, kamfanin na CrowdStrike ya ce ana kan shawo kan matsalar.

Sai dai sa’o’i bayan sanarwa da kamfanin ya fitar, an lura cewa matsalar ta kara ta’azzara.

Fasinja a New York, Amurka
Fasinja a New York, Amurka

A filayen tashin jirage a Amurka, da nahiyar turai da Asiya, rahotanni sun ce an ga dogayen layuka bayan da masu tarbar fasinjoji suka tsaya cik da ayyukansu sanadiyar wannan matsala.

A Australia, matsalar ta tilastawa kafofin yada labarai tsayar da shirye-shiryensu.

A Afirka ta Kudu, ayyukan bankuna sun tsaya sanadiyyar wannan katsewa yayin da a New Zealand hanyoyin biyan kudaden da ke amfani da kati suka samu tangarda.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG