Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Jami'an Kasar Kenya Suke Wa 'Yan Najeriya Kallon Masu Kutse Da Satar Bayanai Na Yanar Gizo; Falz


Shahararren marubin wakokin gambara na turanci kuma mawaki dan Najeriya, Folarin Falana, wanda aka fi sanmi da suna Falz, yayi korafi akan abubuwan da ke faruwa na nuna wariya da bambanci da ake nunawa ‘yan Najeriya wajan shiga kasar Kenya.

Mawakin ya kara da cewa irin babbancin da ya fuskanta yayinda yake ziyara a kasashen gabashin Afirka a kwanakin nan na ci masa tuwo a kwarya.

Mujallar Daily Post, ta bayyana cewa mawakin Flaz, da yake jawabi a ranar lahadin data gabata ya bayyana bakin cikinsa akan yadda aka ware su gefe guda ayayinda suka isa filin jirgin kasar Kenya tamkar wasu bakin haure da ba ‘yan Nahiyar Afirka ba, inda ya bayyana cewa jami’an shigi da ficin kasar sun yi masu kallon masu kutse da satar bayanai ta yanar gizo.

Matashin ya kara da cewa “ina matukar mamakin yadda ake wa’yan Najeriya mazauna kasar Kenya kallon masu kutse da satar bayanai ta yanar gizo”

A cewarsa, daga sauka filin jirgin kasar a hanyarsa ta zuwa ziyara tare da abokan sana’arsa, sai kawai aka kebesu waje guda tamkar wasu bakin haure daga wata Nahiya, inda akai ta yi masu kallon masu kutse da satar bayanai ta yanar gizo.

Daga karshe ya bayyana cewa “gaskiya haka bai dace ba, daga ganin dan Najeriya kawai sai a dakeshi a matsayin mai satar bayanai ta yanar gizo, wannan ai cin fuska ne”.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG