Manyan kamfanonin fasaha na Amurka biyu Google da Microsoft sun amince da wata yarjejeniya da gwamnati don taimakawa wajen gano masu satar fasahar fina finai da wakoki a kan yanar gizo.
Kamfanonin dai sun amince zasu hada kai da gwamnati wajan gano duk masu sauke fina finai ko wakoki ba tare da izini ba. wannan kuwa ya biyo bayan kwashe shekaru da kamfanonin tallata wakoki da na fina finai su kayi suna neman a dakatar da satar fasaha da ake musu.
Inda har suka aka zargi Google da Microsoft da cewa suna rufe idanunsu yayin da ake musu satar fasaha, kuma suna jan ‘kafa kan matakan da ya kamata ace sun ‘dauka wajen kare satar fasaha a kafofinsu.
Karkashin wannan yarjejeniyar kamfanonin sadarwar sun kuduri aniyar dakile duk wasu shafukan yanar gizon da ake amfani da su wajen aikata wannan laifi, ta yadda idan mutane suka yi bincike a shafin bincike na yanar gizo ba zasu fito ba.
Yanzu haka dai kamfanonin zasu saka ido kan masu aikata wannan lefi har na tsawon wasu watanni. Daga baya kuma sai a fitar da hanyar da tafi dacewa wajen magance satar fasaha.