Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaman Lafiya Yafi Zama Dan Sarki


Shirin Fim Din Al'umarmu A Kano
Shirin Fim Din Al'umarmu A Kano

Mubarak Abbah, furodusa a Kannywood, yayi wani sabon fim wanda ke nuna rigiggimu masu nasaba da addini da kuma nuna halaiyar masu rura wutar rikici mai suna “Al’umamu”.

Shi dai wannan fim din makasudinsa in ji Mubaraka shine domin nuna wa jama’a mahimmancin zaman lafiya da kuma nuna hadarin dake cikin rikicin addini wanda baya haifar da alheri ga al’uma.

Mubarak, yace ya fuskancin matsalolin da dama a yayin da nake shirya fim dina mai nasaba da rigiggimu na addini inda ta kai, har sai da ‘yan Sanda suka kama shi a lokacin da suke daukar wani bangare na fim din.

Mubarak ya kara da cewa fim din Al’ummar mu yayi duba dangane da matsalolin da da al’ummar da suka fuskanci matsalolin yaki a yankunansu.suka samu kansu a ciki.

Ya ce fim din yayi nuni da fatara da talauci da rasa rayuka da rikice-rikicen yaki ke haifarwa.

Ya kara da cewa fim din yayi kokarin nuna faruwar yanayi a zahiran yadda mai kallo zai fahimci matsalolin da ake son nuna masa.

Baya ga matsalar da suka samu daga wajen ‘yan sanda, ya ce sun kuma fuskanci matsalolin daga wasu daga cikin jarumai Kannywood inda suke zaton fim din shirin gwamnati ne suka kuma bukaci da sai an yi musu biya mai tsoka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:51 0:00

XS
SM
MD
LG