ABUJA, NIGERIA - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da Olukayode Ariwoola a matsayin sabon alkalin alkalan kasar na riko ‘yan sa'o'i bayan da tsohon babban mai shari’a Tanko Muhammed ya yi murabus.
A wajen bikin rantsuwar, shugaba Buhari ya fadi cewa ya samu wasikar murabus din Tanko Muhammed ranar Litinin, wanda dama ya kamata ya yi ritaya daga kotun kolin a karshen shekarar 2023.
A shekarun aluf dari tara da sittin ne dai aka haifi Ariwoola, ranar 22 ga watan Agusta a garin Oluwoye da ke karamar hukumar Iseyin a jihar Oyo inda kuma ya yi karatun firamare a makarantar gwamnati ta demonstration da ke garin tsakanin shekarar 1959 zuwa 1967.
Ya yi karatun gaba da firamare a makarantar Muslim Modern School ta garin nasu a tsakanin shekarar 1968 zuwa 1969 kafin ya wuce makarantar Ansar-Ud-Deen da ke garin Saki na karamar hukumnar Oyo ta arewa.
Ariwoola ya fara aiki a matsayin mai ba da shawara kan harkokin bautar kasa wato NYSC na jiha a ma’aikatar shari’a ta birnin Akure a jihar Ondo sannan ya zama jami’in shari’a a ma’aikatar shari’a ta jihar Oyo har zuwa shekarar 1988 inda a kashin kansa ya bar aikin gwamnati don bude kamfanın shari’a na kansa.
Mai shari’a Ariwoola ya yi aiki a matsayin Lauya a ofishin aikin lauya Cif Ladosu Ladapo mai mukamın SAN tsakanin watan Oktoban shekarar 1988 zuwa Yulin 1989 lokacin da ya kafa nasa ofishin mai suna Olukayode Ariwoola & Co - kamfanin lauya da masu ba da shawara a garin Oyo a watan Agustan shekarar 1989, daga nan kuma aka nada shi a watan Nuwamban shekarar 1992 a matsayin Alkalin Alkalan Jihar Oyo.
Hakazalika, mai shari’a Ariwoola ya taba zama Alkalin Kotun daukaka kara ta Najeriya, kuma a ranar 22 ga Nuwamba shekarar 2011 aka nada shi a matsayin alkalin kotun kolin Najeriya, wanda tsohon babban jojin Najeriya ya rantsar da shi.
A yanzu dai mukaddashin alkalin alkalan Najeriya da shugaba Buhari ya nada na jiran amincewar majalisar dattawan Najeriya bayan murabus din Mai Shari’a Tanko Muhammad.
A ranar 25 ga watan Janairun shekarar 2019 ne shugaba Buhari ya rantsar da tsohon babban alkalin alkalan kasar, mai sharia Tanko Muhammad wanda ya yi murabus.