Wani fasto a nan Amurka yace ba ya da niyyar janye shirinsa na kona al-Qur'ani Mai Tsarki a kofar cocinsa dake Jihar Florida ranar asabar 11 ga watan Satumba, duk da tofin Allah tsinen da shugabannin addini da na siyasa suka yi da wannan aniya ta sa.
Fasto Terry Jones ya vce lokaci yayi na abinda ya kira samo sabuwar hanyar takalar ta'addanci.
Yace shirinsa na kona abu mafi Tsarki ga al'ummar Musulmi, yana yi ne da 'yan tsagera, kuma yana da goyon baya mai yawa a cewarsa.
Cocinsa dai tana da membobi 50 ne kawai.
A ranar laraba Sakatariyar Harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta ce abin takaici ne ganin cewa wannan fasto dake jagorancin wata 'yar karamar coci ya samu nasarar janyo hankalin duniya da irin wannan abinda ta bayyana a zaman abin kunya.
Wani kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, yace wannan mataki na faston zai raunana yunkurin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afghanistan.
Fadar Paparoma Benedict ta Vatican, tayi Allah wadarai da wannan yunkuri na kona al-Qur'ani, tana mai bayyana shi a zaman abin fushi, kuma abu mai muni.
Shi ma sakataren Kungiyar Kiristoci ta Najeriya a jihohi 19 na arewacin kasar, Reverend Sa'idu Dogo, ya nuna fusata da wannan matakin, yana mai cewa yin hakan ya saba da ka'idojin addinin Kirista.