Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Jefa Bam A Ofishin Jam’iyyar APP A Fatakwal


Gwamnan jihar Rivers a Najeriya, Siminalayi Fubara (Hoto: Facebook/Fubara)
Gwamnan jihar Rivers a Najeriya, Siminalayi Fubara (Hoto: Facebook/Fubara)

Harin na zuwa ne yayin da ake ta rade-radin cewa Gwamna Siminalayi Fubara na shirin komawa jam’iyyar ta APP.

Da sanyin safiyar ranar Litinin wasu mahara da ba a san ko su waye ba, suka jefa wani abin fashewa a hedkwatar jam’iyyar Action Peoples’ Party (APP) da ke birnin Fatakwal a jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya.

Rahotanni sun ce babu wanda ya jikkata, amma harin ya lalata wasu sassan ginin hedkwatar jam’iyyar wanda ke yankin GRA a birnin.

Harin na zuwa ne yayin da ake ta rade-radin cewa Gwamna Siminalayi Fubara na shirin komawa jam’iyyar ta APP.

Fubara ba sa ga maciji da tsohon gwamnan jihar ta Rivers kuma Ministan birnin Abuja, Nyesom Wike wanda dan jam’iyyar PDP.

Wike ya taka muhimmiyar rawa a darewar Fubara karagar mulkin jihar karkashin jam’iyyar ta PDP, sai dai manyan ‘yan siyasar biyu sun samu sabani a baya-bayan nan.

Harin har ila yau na zuwa ne yayin da jihar ta Rivers ke shirin gudanar da zaben kananan hukumomi inda wasu suka danganta harin da zaben dake tafe.

Jaridun Najeriya da dama da suka ruwaito labarin harin sun ce wasu sassan rufin ginin ofishin jam’iyar ta APP sun lalace.

Bayanai sun yi nuni da cewa an kai harin ne da misalin karfe uku na dare.

Babu dai wanda ya dauki alhakin harin, amma mutane da dama na cewa bai rasa nasaba da takaddamar siyasa da jihar ke fama da shi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG