Rikicin siyasa da ya bullo a jihar Rivers tsakanin gwamnati mai ci da kuma magoya bayan tsohuwar gwamnati, ya dauki hankali a fadin Najeriya, lamarin da ya sa shugaban kasa gayyatar dukkan bangarorin domin zaman sulhu.
Halin da ake ciki dai za a iya cewa an cimma matsaya a taron, inda dukkan bangarorin da aka gayyata suka tattauna tare da samar da wasu sharudda da ake sa ran za su tabbatar da zaman lafiya.
Cikin sharuddan da aka samar, ‘yan majalisa da suka fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC maimakon a kore su za su koma bakin aikinsu a Majalisa. Haka kuma yunkurin tsige gwamna da Majalisar ta fara za ta dakatar da shi.
Haka kuma an cimma matsayar cewa kwamishinoni da suka ajiye aiki za su koma bakin aiki. Shi kuma gwamna Mista Fabura zai sake aikawa Majalisa kasafin kudin da suka ki kulawa.
Wakilin sashen Hausa a Abuja Umar Farouk Musa, ya tattauna da jami’in yada labarai a fadar gwamnatin Abdulaziz Abdulaziz, domin jin yadda shugabsa Tinubu ya yi nasarar sasanta wannan rikici musamman duba da cewa jihar ta jam’iyyar adawa ta PDP ce.
Dandalin Mu Tattauna