Abu mafi mahimmanci da taron ya jaddada shi ne samarwa matasa ayyukan yi tare da kawo abubuwan da zasu farfado da jihar cikin gaggawa.
Ministan ilimi mai zurfi na kasar Nijar Yahuza Sadisu Namadubi shi ya rufe taron tare da yin alkawarin gabatar da duka shawarwarin da aka cimma wa mahukuntan kasar domin su duba yadda zasu gudanar dasu.
Kaka Tuda wani matashi daga jihar Diffa din ya kira a yi aiki da duka shawarwarin da aka bayar saboda irin matsalolin da matasa ke ciki. Ya roki jama'a jihar su yi hakuri. Wadanda aka kashe 'ya'yansu su yi hakuri su yafe. Rashin aiki da rashin ilimi ya sa 'yan ta'adda ke samu suna yaudarar matasa.
Musa Tangari na wata kungiya yace tun da aka gano bakin zaren matsalolin daukan matakan da suka dace ya rage ga hukumomin kasar. A yi tsari nagari bisa adalci da gaskiya tare da damawa da mutane.
Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.
Facebook Forum