Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Ce Shedan Ne Yasa Shi Yi Wa Uwa Da 'Yar Ta Fyade


Jail
Jail

Jami'an tsaron 'yan sanda a jahar Naija sun kama wani matashi mai suna Yusuf Suleiman dan shekaru 25, da zargin yi wa wata yarinya 'yar shekaru biyu da rabi fyade a garin Dutsen Kura dake babban birnin jahar.

Kamar yadda mujallar Vanguard ta wallafa, An zargi matashin da yi wa mahaifiyar yarinyar fyade a shekarun da suka gabata.

A yayin da matashin ke amsa tambayoyi gaban manema labarai a harabar shalkwatar 'yan sandan jahar da ke Minna, Yusuf Suleiman ya amsa aikata laifin inda ya danganta lamarin da cewa aikin shedan ne.

Mai Magana da yawun 'yan sandan jahar ASP Bala Elkana ya fada wa manema labarai cewar matashin ya bayyana cewar ya ga lokacin da yarinyar 'yar shekaru biyu da watanni da haihuwa ta fito daga gidan su ita kadai, ya kuma dauke ta zuwa wani lungu inda ya yi mata fyade.

Elkana ya ce za'a tura matashin zuwa kotu da zarar sun kammala sauran binciken da suke kan kaddamar wa.

Mahaifiyar yarinyar mai suna Zainab a gajerar hirar da tayi da 'yan jarida ta bayyana cewa bata taba amincewa da abutar da mijinta ke yi da Yusuf Suliman ba, dalili kuwa shine ya yi mata fyade a lokacin da take misalin shekaru goma da haihuwa amma bata fadawa kowa ba.

Ta kara da cewa shekaru goma da suka gabata ya kaita wani wuri da suke wanke babur a wata kwana ya yi mata fyade.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG