Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kishin Kwaliya Tsakanin 'Yan Mata A Taro


A shirin mu na yau, dandalinvoa ya waiwayi batun nan na yan Mata idan sun kure adaka suka kuma fito tas a wuraren biki ko suna ko ma duk wani wajen taron na Mata da zarar sun ga wacce ta fi su kwaliya suke shan jinin jikinsu

Wannan dai na daga cikin dabi’un 'yan Mata na so a nuna cewar sun fi kowa kyau a sa’oinsu na 'yan mata, da zarar sun ga akasin haka sai fuskarsu ta canza ko su daina walwala

Da wannan batu ne dandalinvoa ya zanta da wasu matasan 'yan Mata masu jini a jiki wanda suke bayyana cewa “burin kowacce diya mace dai bai wuce ta kece raini tsakanin sa’ointa a taro ko duk wani wajen da ya hada taron mata

Sun kara da cewa da zarar ka ga wanda ta fi ka kyau toh lailai akwai damuwa domun hankula ilahirin jama’a zai koma kan wacce ta shigo ta kuma dau wanka musammam ma wajen akwai taron samari

Ku biyo mu domin jin wannan muhawarra.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG