WASHINGTON D.C —
Idan kana da shafi a Facebook da Twitter, kuma kana son rubuta wani labari, ko saka wani hoto a dukkan shafukan biyu, amma kana gudun sai ka bude wannan ka saka, sannan ka bude wancan ma ka saka, to akwai hanyar kauce ma hakan. Zaka iya sanya labari ko hoto a kan shafinka na Twitter kuma ya fito a shafinka na Facebook ba tare da sai ka bude Facebook din ka sanya ba.
- Abinda zaka yi da farko shine ka shiga shafinka na Twitter a kan kwamfuta. Idan da waya kake amfani, kana iya bude Twitter din a cikin Browser ko manhajar bude intanet, sai ka duba a kasa inda aka ce “GO TO DESKTOP SITE” ko kuma “GO TO FULL SITE”.
- Idan ka bude Twitter din ta wannan hanya, sai ka matsa inda hotonka yake na shafin, watau Profile Image a turance, a can gefen dama a saman shafin, idan ya bude maka abubuwan da zaka iya zaba, sai ka matsa inda aka rubuta SETTINGS.
- Sai ka duba kasa a gefen hagu na shafin da ya bude, ka je kasa ka matsa inda aka rubuta APPS.
- A shafin da zai bude maka, sai ka matsa inda aka rubuta “CONNECT TO FACEBOOK”
- Daga nan zaka ga wani shafi karami ya bude a tsakiyar kwamfutar yana neman ka sanya bayanin da kake amfani da shi wajen shiga Facebook, watau suna ko adireshin email da kuma mabudin shiga ko Password. Sai ka rubuta a nan, sannan ka matsa inda aka rubuta “OKAY”
- Daga nan sai ka zabi wadanda kake son su rika ganin abubuwan da kake sanyawa a Facebook din naka kamar yadda kake yi idan ka shiga Facebook kai tsaye, sannan ka matsa “”OKAY”
Shike nan ka gama! Daga wannan lokacin, duk abinda ka rubuta a shafinka na Twitter, zai bayyana a shafinka na Facebook. Watau dai, ka tauna taura biyu ke nan a lokaci guda.
A kashi na biyar dake tafe, zamu bayyana muku yadda mutum zai iya kofe na dukkan abinda ya taba sanyawa a shafinsa na Facebook, har ma da wadanda ya manta da su shekaru masu yawa da suka shige.