Watan Ramadanawatan watan rahama, kuma watan da kowane bawa yake neman ‘yantuwa zuwa ga rahamar Allah. Don haka wannan wata ne da yakamata ace kowane mahaluki yayi amfani da wannan damar don samun falalar da ke tattare a wannan watan, musamman ma masu hannu da shuni, gwamnatoci, ‘yan kasuwa da ma daukacin al’uma, wajen neman dacewar da rahamar Allah.
Babban abun da yakamata ace mutane su maida hankali a kai shine su dinga saukaka kayan masaruhi a cikin wannan watan, domin duk wanda ya saukaka ma wani to insha Allah shima zai ga sakamako wajen Allah, ba lallai sai mutun ya baka kyauta ne kawai zai iya samun lada a wajen kaba, harma wanda ya saukaka ma mutane wajen samun abubuwan more rayuwa cikin sauki na iya samun rahamar mai duka.
Ashe kuwa yakamata mutane su kwadaita kansu da neman wannan rahamar. Tabakin Malam Shamsu Da’u, wani mai sana’ar gidan gona, ya bayyanar da yadda suke kokarin rage kudin kajinsu don mutane su samu damar iya siyanwadannan kayan cikin rahusa, don suna kokarin su samu wannan falalar ta watan Ramadana. Suna kuma kara kira da sauran ‘yan kasuwa da su yi kokari wajen rangwanta ma jama’a wajen samun albarkar da ke cikin wannan watan, don kuwa duk wanda yabi karamar riba da niyyar taimaka ma al’uma to bashakka zai samu dacewa da wannan rahamar dake cikin watannan mai albarka.