Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashin Farashin Kayan Masarufi a Lokacin Azumi


Women sell vegetables and other food in a market on World Food Day in Lagos, Nigeria, Tuesday, Oct. 16, 2012. One in eight people around the world goes to bed hungry every night, according to the United Nations.
Women sell vegetables and other food in a market on World Food Day in Lagos, Nigeria, Tuesday, Oct. 16, 2012. One in eight people around the world goes to bed hungry every night, according to the United Nations.

Yau ne al’umar musulmin duniya suka fara azumin watan Ramadan bayan cikar watan Sha’aban kwanaki 30 a jiya Laraba. Sai dai Azumin Ramadan na bana ya sami mutane cikin kalubalen rashin kudi da tashin gwauron zabin farashin kayayyakin masarufi na yau da kullum.

Kamar yadda wani daga cikin masu sana'ar kayan gwari, wato kayan miya irin su tumaturi da sauran su ya bayyana, dalilin tsadar wadannan kaya a wannan lokaci shine rashin samun kayan a inda ake noma su a sakamakon rashin zuwan ruwan sama da sauri.

Malamin ya kara da cewa ko dashike farashin ya dade da tashi tun kafin zuwan azumin amma bai kai kamar yadda suke sayar da shi yanzu ba.

Malamai a wurare da dama sun fara yi wa jama'a nasiha musamman akan muhimmancin taimakawa jama'a a wannan wata mai alfarma, kuma sun yi kira ga masu sana'a da su taimakawa jama'a domin samun taimako daga subuhanahu wata'ala.

Ga Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.

XS
SM
MD
LG