Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kasuwanci ta Duniya Na Bukatar Sabon Salon Gudanarwa-Dr. Ngozi


Ngozi Okonjo-Iweala.
Ngozi Okonjo-Iweala.

Sabuwar shugaban Kungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO) ta ce a wadannan lokutan da ke cike da kalubale, ba za a ci gaba da tafiyar da ayyuka kamar yadda aka saba ba,” tana mai cewa “ana bukatar sake fasali mai zurfi da fadadawa” a tsakanin kungiyar kasuwanci ta duniya da kanta.

Sabuwar Darektar Kungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO) da aka nada Ngozi Okonjo-Iweala ta ce yayin da kaskancin kai ta ke alfahari da kafa tarihi da ta yi, yana da muhimmanci a samu kwarewar gabatar da sakamako.

“Ina maida hankali kan cika aiki da kuma samun sakamako. Kuma ina so in tabbatar da cewa mutane sun tuna nahiyata da ta samar da shugabar kungiyar WTO ta farko da ta kawo canji. ”

Okonjo-Iweala ta ce kasuwanci ya shafi mutane ne hade da daga wadanda aka ware, kamar mata da masu kananan masana'antu don a dama da su.

’Yar Najeriya Nkoyo Toyo, tsohuwar‘ yar majalisar dokoki ce kuma tsohuwar jakadiya a Habasha da Tarayyar Afirka, ta yi aiki tare da Okonjo-Iweala kuma ta ce ita ‘yar sahun gaba ce” Ita wata mutumiya ce wanda ta kasance babbar mai kirkire-kirkire. Tace Ngozi, tunanin ta shi ne, abun da zan iya yi daban kuma wane canji zan iya kawowa a lokacin mawuyacin yanayi."

Karin bayani akan: Ngozi Okonjo-Iweala, WTO, Nigeria, da Najeriya.

XS
SM
MD
LG