Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Na Taya Okonjo-Iweala Murnar Zama Shugabar WTO


Dr. Ngozi Okonjo-Iweala
Dr. Ngozi Okonjo-Iweala

Muna taya sabuwar shugabar WTO, Okonjo-Iweala, murna.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta taya Dr. Okonjo-Iweala, murnar samun nasara, a cikin wata sanarwa da fadar ta fitar dauke da sa hannun Kakakin shugaba Buhari, Malam Garba Shehu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kwatanta Dr Okonjo Iweala a matsayin kwararriya a fannin tattalin arziki, wacce ta yi karatu a Jami’ar Havard, inda ya kara da cewar, tana da kwarewar da za ta kai duniya ga gaci.

Ya kuma ayyana cewa, tarihin da ta kafa wajen rike gaskiya da burin ganin ci gaban al’uma, zai ci gaba da sama mata mafita a harkokinta na rayuwa, da kuma yadda za ta taimakawa al’umar duniya.

Ngozi Okonjo-Iweala shugabar WTO
Ngozi Okonjo-Iweala shugabar WTO

Shugaban na Najeriya ya kuma yi fatan cewa, Dr. Okonjo Iweala, wadda ta taka rawar gani wajen samar da sauye-sauye a fannin tattalin arzikin Najeriya, a mukaman da ta rike na Ministar Kudi da ministar harkokin waje, zai ba ta damar da za ta yi zarra a wannan sabon mukami, nata tare da inganta wannan nauyi da aka dora mata na samar da daidaito a cibiyoyin kasuwanci na duniya ta yadda kowa zai amfana.

Shugaba Buhari ya ce yana mai bin sahun iyalai, abokanai da takwarorin aikinta, wajen yi mata fatan alheri a wannan sabon mukami da ta samu.

Karin bayani akan: Ngozi Okonjo-Iweala, WTO, Nigeria, da Najeriya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG