Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Samo Wasu Daga Cikin Bangarorin Jirigin Kasar Masar



A truck, carrying mostly Honduran migrants taking part in a caravan heading to the U.S., passes by a wind farm on the way to Juchitan, near the town of La Blanca in Oaxaca State, Mexico.
A truck, carrying mostly Honduran migrants taking part in a caravan heading to the U.S., passes by a wind farm on the way to Juchitan, near the town of La Blanca in Oaxaca State, Mexico.

Kwamitin da ke binciken jirgin saman kasar Egypt, da ke dauke da mutane sittin da shida 66, wanda ya fada cikin tekun “Mediterranean” a watan da ya gabata. Sun bayyanar da samar da wasu bangarorin jirgin. Sun bayyanar da cewar kamfanin “John Lethbridge” da aka dauka haya don neman jirgin sun bada gudunmawa matuka.

Sun bayyanar da wasu gurare da burbushin jirgin suka makale a cikin tekun, suna kuma kara zurfafa bincike don bayyanar da iya abun da suka samo. Shi dai jirigin “EgypyAir Airbus A320” yana kan hanyar shi ta zuwa kasar Masar dinne daga kasar Paris, wannan abun ya faru da shi.

A ranar shatara ga watan Mayu ne wannan jirgin ya hadu da wannan musibar. Wasu daga cikin sakamakon binciken su, ya bayyanar da cewar jirgin yayi shawagi kamin ya rasa hanyar shi. Daga bisannin kuwa sai wasu ingina suka fara hayaki kamin matuka jirgin suka rasa damar juya jirgin zuwa hanyar da ta kamata.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG