A ci gaba da wannan canji na Nishadi, bugu da kari, za mu yi hira da jama'a game da yadda suke kallon al'adun Bahaushe da yadda aka samu canji a ciki.
Wakiliyar DandalinVOA yau ta yi hira da wani marubuci, da kuma wasu matasa, don jin tabakinsu kan karatun littafan Hausa ko akasin haka.
Daga cikin wadanda suka yi bayani, wasu sun ce, da suna karatun litattafan Hausa sai dai yakan dauke musu hankali wajen mayar da hankali ga harkar karatunsu na boko ko na Qur'ani.
A hirar wakiliyarmu kuwa da Nazir Adam Salihi, marubucin litattafai na Hausa, wato kagaggun labarai na al’ada, ko soyayya, wanda a da kafin shigowar wayoyin zamani ya zamanto wata hanya ta nishadantarwa game da ilmantarwa, marubucin ya ce shigowar wayoyin sadarwa sun haifar da koma baya ga littatafan Hausa.
Marubuci Nazir ya fara rubutu tun a shekara ta 1989, amma littafinsa bai fara fita ba sai a shekara ta 1986, a lokacin ne mutane suka fara karanta littafin, inda aka faro da littafin ‘Kibiyar Ajali’.
Ya ce marubuta suna nan suna kokarin fitar da manjahaja da za ta saukakawa 'yan zamani karatun litattafan Hausa ta amfani da wayoyinsu ko kafofin sadarwa cikin sauki, wanda hakan zai ci gaba da daga martabar kasar Hausa da al’adunsu da sauransu.
A saurari cikakken rahoton wakiliyar Muryar Amurka Baraka Bashir.
Facebook Forum