'Ya'yan kungiyar da aka fi sani da BringBackOurGirls sunce zasu cigaba da zaman dirshen, sannan zasu yiwa manema labarai jawabi da karfe hudu na yamma musamman saboda mayar da martani ga wasu kalamai da shugaban kasa yayi a lokacin da ya gana ‘yan jarida, inda yake cewa nan da makonni 6 za’a kwato daliban Chibok. To shine wannan kungiya tace a yau, idan tayi zamannan, zata fara kidayar kwanaki har zuwa cikar makonnin shidannan, da shugaban kasa ya fadi da bakinsa.
Yanzu dai masu zaman dirshen sun share watanni 9 da kwanaki 15 dai-dai da fara zaman BringBackOurGirls, kuma kowace rana sai sun fito. Sun bayyana a dukka rahotanni cewa baza su fasa wannan zama ba, koda mutum daya ne zai rage, har sai ranar da gwamnati ta kwato yaran, ko suna raye, ko kuma a kawo gawarwakin wadanda suka mutu.
A halin yanzu rabin iyalan daliban Chibok sun bar-bazu a cikin birnin Abuja, akwai matsuguni har wajen shida da iyaye da ‘yan uwa suke fakewa, biyo bayan hare-haren Boko Haram akan garuruwansu.
Ranar 14 ga watan Afrilu ne aka sace wadannan dalibai su kusan 300 a lokacin da suke rubuta jarrabawar karshe ta fita daga sakandare.
An sanar da rundunar sojin Najeriya akan cewa mayaka sun nufi garin Chibok, amma basu dauki matakin kare garin ba, balle ceto daliban da mayaka suka share makonni suna yawo da su a Jihar Borno.
Ya dauki gwamnatin Najeriya makkonni uku kafin a hukumance ta amince an sace wadannan dalibai, sannan ya zuwa yanzu, Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya bai ziyarci garin Chibok ba.