A Nijeriya, malaman Addinai da yan Kungiyar Bring Back Our Girls masu fafutukar ganin an kwato ‘yan matan Chibok, wadanda ‘yan Boko Haram su ka sace su a bara, sun gargadi ‘yan siyasa da su kauce wa amfani da Kalaman Kawo rarrabuwar kawunan ‘yan kasa; sun kuma yi wa Gwamnati tuni akan batun ‘yan Matan Chibok da yan ta'adda suka sace yau watanni kusan tara Kenan. Sun yi wadannan kiraye-kirayen ne a wani taron bukin Sabon Shekarar Miladiyya a Abuja.
Wakiliyarmu a Abuja wadda ta turo ma na da wannan rahoton, Madina Dauda ta ruwaito Limamin Kirista Reverend Daniel Yusufu Nbaya na Majami’ar EYN da ke Utako na Abuja na cewa, “kullum abin da na ke gaya wa jama’a shi ne mu sa kasarmu farko – Ubangiji shi ne na farko, amma kasarmu ta biyo baya. Mu na nan fa domin kasarmu ne. Idan babu kasarmu babu mu. Ba za mu je wata kasa mu zama masu kasar ba; in mun je wata kasa mun zama baki. Ya kamata mu kasance da bangaskiya cewa kasarmu za ta fita daga wannan kangin; za ta fita kuma da daraja; za ta fita kuma har mutanen waje su yi marmarin zuwa amma ba wai mu ne kawai za mu rinka kwakwazon zuwa wasu kasashe ba. Mu cigaba da addu’a da zama masu biyayya da doka; mu rinka addu’a domin kasar da kuma shugabanni.”
Madina ta yi nuni da yadda mata da dama su ka zama gwauraye, yara da yawa kuma su ka zama marayu tun bayan dawowar dimokaradiyya sakamakon tashe-tashen hankulan sisaya, wadanda akan danganta su da matasa, wadanda ake zargin ana amfani da su wajen kai hare-hare. Wannan, a cewar Madina Dauda, ya sa Shugaban Kiristan Nijeriya shiyyar Matasa (Youth-CAN), injiniya Daniel Kazzai ya ki kiran cewa ya kamata a kirkiro hanyar fayyace ma matasa muhimmancin zama lafiya a Nijeriya. Y ace ya kamata a yaki duk wanda ke kokarin raba kasar.
Shi kuwa Malam Dauda Iliya, Sakataren Kungiyar ‘yan asalin garin Chibok mazauna Abuja, y ace lallai kungiyarsu na boyon bayan kungiyar fafatukar Kwato ‘yan matan Chibok da ake wa lakabi da BringBackOurGirls. Y ace batun wajibcin dawo da ‘yan matan Chibok din zai yi tasiri sosai a zabe mai zuwa. Y ace duk wanda zai nemi kuri’ar ‘yan Chibok sai ya yi zancen ‘yan matan da aka sace don su san ko ya cancanta su zabe shi ko a’a. Amma y ace sun a da kwarin gwiwar cewa za su iya zabe a 2015 saboda an tsara yadda za su yi zaben ko da bas u zaune cikin garin na Chibok. Kakain hukumar zabe Nick Dazang ya tabbatar cewa lallai an tsara yadda kowa zai sami damar kada kuri’arsa.