‘Yan gwagwarmayan kwato ‘yan matan Chibok, a karshen mako ke kara kaimi ga kamfe din neman dawo da matan, tun sace su kusan wata bakwai, da suka gabata.
Shugaba Jonathan da jami’an Gwamnatin sa sun sha’alwashin dawo da matan, har ya kai ga wata yarjejeniyar, tabbatar da haka, amma da alamun zuwa yanzu ba’a gano bakin zaranba ko kuwa bakin zaran ya sake bacewa a taron kukumadi.
‘Yan kungiyar suka ce zasu matsa kaimi har shi kansa shugaba Jonathan, ya fito sun tasashi a gaba don karbo matan, suka kara da cewa ba zasu daina wannan gwagwarmayar ba har sai haka ta cimma ruwa.
Hadiza Bala Usman, daya daga cikin shuwagabanin kungiyar,tace babu wani alamu daga Gwamnati, cewa su nayin wani abu akan ceto ‘yan matan nan.
Ta kara da cewa ranar laraba ‘yan kungiyar za suyi tattaki zuwa ofishin jakadancin Chad, domin jin ba’asin inda aka kwana dangane da kwato ‘yan matan na Chibok.