Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Watan Ramadan Na Cike Da Darussa, Har Zuwa Sauran Watanni


Malam Nuhu Muhammad Usaini
Malam Nuhu Muhammad Usaini

Kamar yadda masu iya magana kan ce shekara kwana, tuni aka kawo gangara na azumin watan Ramadana. Hakan yasa DandalinVOA waiwayar ire-iren darussan da Musulmai suka koya a wannan watan, da kuma yadda ya kamata su jajirce wajen cigaba da kyawawan dabi’un da suka koya a watan na Ramadan.

Mun kuma zanta da Malam Nuhu Muhammad Usaini, Limamin Massallacin Kafalatul Islamiya, dake jikin gidan radiyo a unguwar Tukuntawa dake Kanon Najeriya, wajen ganin an taimakawa miskinai a wannan lokaci.

Ya ce ana so musulmi ya kasance ayyukan da ya ke aikatawa a watan Ramadana ya zama mai juriya wajen aikata shi har bayan watan, yin hakan ne ya ke tabbatar da cikar imanin musulmi na kwarai mai jajircewa da ibada.

Malamin ya kara da cewa ciyarwa na da matukar muhimmanci a lokacin azumi, da bayan azumin watan, kuma nasiha ce mai inganci ga dukkanin musulmi ya kamata ya kasance yana yi.

Daga nan kuma har yanzu akan darussan da ake koya a watan na ramadan, Malam Muktar Umar Sharada, limamin masallacin juma’a na Rijiya Zaki ya kara yin tsokaci, inda ya ce ana koyon hakuri, juriya da yakana.

A saurari rahoton wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:33 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG