Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Buhari Zata Fara Biyan Alawus Ga Talaka


 Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

A Najeriya, Gwamnatin kasar ta fara bayar da tallafin kudi Naira dubu biyar biyar ga marasa aikin yi domin taimakamasu kamar yadda Gwamnatin kasar tayi alkawari a baya jihar Neja, na daya daga cikin jihohi tara da aka tsara zasu fara cin gajiyar shirin daga wanna watan na janairu.

Jami’in shirin a jihar Neja, Akilu Musa Kuta, yace anyi shirin yadda za’a fara bada kudaden ta Banki, a kananan hukumomin da aka tsara za’a fara bada kudaden a kashin farko domin gudun samun wata matsala.

Musa Kuta, ya kara da cewa an kammala daukar kididdiga, kuma daga banki, zasu karbi kudadensu, yana mai cewa akwai gidaje fiye da dubu goma da dari daya da zasu amfana da wanna tallafi na Gwamnati.

Afinic Dauda, ta hukumar N POWER, a jihar Neja, tace wannan al’amari abin godiya ne ganin yadda alkawarin Gwamnatin Najeriya, ke shirin cika.

Dan majalisar dokokin jihar Neja, Bello Agwara, wanda shima ya bada tallafin kudi kimanin Naira miliyan bakwai, ga wasu al’umar mazabarsayace shirin bada kudade ga jama’a, na taimakawa wajan rage radadin talauci a tsakanin al’uma.

Masu nazarin al’amura na gani cewa samar da aikin yi a tsakanin matasan da kuma bunkasa masana’antu, a kasa shine yafi mahimmanci.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG