Kwanaki biyu bayan faduwar tankar mai a Dikko Junction da ke yankin Suleja a jihar Nejan Najeriya, wata tanka dauke da man gyada ta fadi a yankin Bida.
Duk da asarar rayuka mai yawa da aka yi a hatsarin farko, mazauna garin sun sake jefa rayukansu cikin hadari ta hanyar kwasar man gyadan daga wurin hatsarin da ya faru a ranar Litinin.
Wasu hotunan bidiyo da suka karade shafukan sada zumunta sun nuna yadda maza, mata da yara suke tururuwar zuwa kwasar man gyadan.
Mutum kusan 100 ne suka rasa rayukansu a hatsarin tankar man da ya auku a Suleja a lokacin da suke kokarin kwasar man fetur a ranar Asabar 18 ga watan Janairu.
Akalla mutum 55 ne suka jikkata. Al’amarin ya faru ne bayan da wuta ta tashi a wajen.
Irin wadannan hadarurruka sun yawaita a Najeriya, musamman saboda cire tallafin man fetur a shekarar 2023, wanda ya haifar da tsadar farashin fetur.
Wannan matsin tattalin arziki ya jefa wasu mutane cikin haɗari ta hanyar tattara mai daga tankar da suka kife don amfani na kai ko sayarwa.
A wani lamari makamancin haka a watan Oktoban 2024, wata tankar mai ta fadi a yankin Majiya da ke jihar Jigawa lamarin da ya lakume rayuka sama da 100.
Dandalin Mu Tattauna