Wata tanka makare da mai tayi bindiga a jihar Jigawa dake shiyar arewa maso yammacin Najeriya.
Al’amarin wanda ya faru akan iyakar Jigawa da Kano, ya jefa wadanda suka shaida hakan cikin firgici.
Jami’in hulda da jama’a na reshen jihar Jigawa na hukumar kashe gobara ta tarayya, Aliyu M.A, ne ya tabbatarwa manema labarai da afkuwar lamarin a yau Laraba, 13 ga watan Nuwambar da muke ciki.
A cewar Aliyu, “ranar 12 ga watan Nuwambar 2024, da misalin karfe 10.43 na safiya, hukumar kashe gobara ta tarayya ta samu kiran gaggawa daga dagacin kauyen Kuho, Zubairu Ahmad, game da hatsarin tankar mai a garin Tsaida dake kwanar kalle, kusa da kauyen Gamoji dake kan titin zuwa Maiduguri.”
Nan take hukumar kashe gobara ta tarayya tayi martani ga kiran, tare da isa wurin da al’amarin ya faru da misalin karfe 10.50 na safiya. An yi nasarar shawo kan gobarar tare da kashe wutar,” in ji Aliyu.
Hakan na zuwa ne wata guda bayan faruwar makamancin hatsarin a watan Oktoban da ya gabata, al’amarin da ya yi sanadiyar asarar rayuka fiye da 170.
Dandalin Mu Tattauna